Matar gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Isma El-Rufai, ta nemi shawarar mabiyanta a shafinta na Twitter akan shin ta fara toshe mutanen da suke damunta ko a’a.
“Na toshe ko kada na toshe? wannan shine tambayar da ta wallafa a shafin nata.
Abin mamaki kuma shine, mijinta, gwamna Nasir El-Rufai yayi sharhi akan abinda ta wallafa din, inda ya ce: “Kada ki toshe su baki daya…ki rufe su za suyi ta ihu ke kuma baki ma san mai suke yi ba.”
Wannan rubutu da Hadiza ta wallafa ya zo ne kwanaki kadan bayan ta nuna farin cikinta da samun sama da mabiya dubu tamanin a shafinta na Twitter, inda su kuma mutanen Kudancin Kaduna suke kuka da kisan da aka yiwa wasu mutane a yankin arewa maso yammacin jihar.
Mutane sun yi caa akan matar gwamnan ne, inda da yawa suka bayyana abinda tayi a matsayin rashin tausayi.
A wani rahoton kuma Press Lives ta kawo muku rahoton mutumin da aka dauka a bidiyo da waya a cikin motar haya yana shafa jikin wata budurwa dake zaune kusa dashi.
An ruwaito cewa an dauki bidiyon ne a lokacin da motar hayar ke kan hanyar zuwa garin Akure babban birnin jihar Ondo, daga babban birnin tarayya Abuja.
Ga dai cikakken labarin da kuma bidiyon yadda lamarin ya faru: Yadda wani fasinjan mota ya dinga shafa jikin wata budurwa a lokacin da suke kan hanyar Abuja