Tsohon Kanal din hukumar sojin Najeriya mai ritaya, Hassan Stan-Labo, a wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels TV, yayi kira da a dinga yankewa ‘yan siyasar da aka kama da laifin satar kudin al’umma hukuncin kisa.

Da yake magana dangane da kara samun karuwar laifuka na cin hanci da ake yi ga ‘yan siyasar Najeriya, tsohon Kanal din sojin yayi kira da a yanke hukuncin kisa kawai akan irin wadannan ‘yan siyasar.

Kanal Hassan Stan-Labo ya bayyana hakane a lokacin da yake amsa tambayar da ake yi masa lokacin hirar da yake a cikin shirin ‘Politics Today’, tare da dan jarida Seun Okinbaloye a gidan talabijin din na Channels TV.

“Ni mai bada babbar shawara ne akan hukuncin kisa a kasar nan, kunga dinga wadannan ‘yan siyasar da suke sace biliyoyin kudaden mu bayan sun yi gwamna, sai su nemi kujerar sanata, da ace an dauki lamarin da gaske, da tuni yanzu mun binne su.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here