Da Jonathan ko wani dan Kudu ne ke mulki da tuni an ce shirya kashe-kashe ake don cutar da Arewa – Sheikh Jabir Sani Mai Hula

0
1518

Fitaccen matashin malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya, Sheikh Jabir Sani Mai Hula, yayi magana akan yadda ake yiwa al’umma kisan kiyashi a yankin Arewacin Najeriya, kuma a lokacin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A wani rubutu da Shehun Malamin ya sanya a shafinsa na Facebook, Malamin yayi tsokaci akan maganganun da mutane suka dinga yi a shekarar 2015 da suke cewa: “An shirya kashe-kashe ne domin a cutar da nahiyar arewa.”

Malamin ya ce wannan magana ba haka take ba.

“Duk karfin magana tana iya zama ba gaskiya ba, tabbas da ace Jonathan ne ko kuma wani daga yankin Kudancin Najeriya yake mulki, da tuni mutane sun fara ‘kashe-kashen nan an shirya su ne don a cuci mutanen arewa.

“Ya kamata mu dauki darasi akan yadda muke zargin jama’a. Allah ya yafe mana kurakuran mu, ya kuma baiwa shugabannin mu kwarin guiwar sauke hakkin da yake kansu, ya kuma kawo mana sauki baki daya.

A ‘yan kwanakin nan dai ana ta samun asarar mutane a Arewacin Najeriya, inda ‘yan bindiga da ‘yan Boko Haram suke kaiwa kauyuka hari daban-daban.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here