Da duminsa: Za a fara daukar sababbin ma’aikatan N-Power ranar 26 ga wannan watan

0
743

A ranar Juma’a 19 ga watan Yuni ne, ma’aikatar jin kai da walwalar jama’a ta kasa ta sanar da ranar da za a fara daukar sababbin ma’aikatan N-Power a Najeriya.

Sadiya Umar Farouq ita ce ta bayyana haka, inda ta ce za a bude shafin yanar gizo a ranar 26 ga watan Yuni, domin mutane su shiga suyi rijista, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Haka kuma Ministar ta bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta sallami rukunai biyu da ta fara dauka a shekarun 2016, da 2018, inda ta bayyana cewa za a sallamesu a ranar 30 ga wannan watan da kuma ranar 31 ga watan Yuli.

Ministar ta ce tuni gwamnatin tarayya ta fara sauya tsarin rukunnan guda biyu zuwa tsarin kasuwanci.

“Mun fara canja tsarin ma’aikatan rukunan guda biyu zuwa tsarin kasuwanci, haka kuma zamu sanya ma’aikatu na ‘yan kasuwa dana gwamnati su dauki wasu daga cikinsu aiki bayan mun kammala gwada kwarewar su a fannoni daban-daban.

Sadiya ta kara da cewa: ‘Gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen cigaba da fadada wannan tsari, hakan ne ma ya sanya yanzu take shirin daukar wasu sababbin ma’aikatan.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here