Da duminsa: ‘Yan bindiga sun kashe sama da mutane 50 a jihar Sokoto

0
293

Sama da mutane 50 ne aka kashe a wani hari da ‘yan bindiga suka kai kauyukan Garki, Katuma da Kuzari dake cikin karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto, a ranar Laraba 27 ga watan Mayu, 2020.

A yadda rahoto ya nuna ‘yan bindigar sun shiga kauyen da misalin karfe 6 na yamma, suka dinga harbin kan mai uwa da wabi a kauyukan.

Wadanda suka samu raunika tuni an garzaya da su asibiti suna karbar magani, inda wadanda suka riga mu gidan gaskiya kuma aka ajiye su a dakin ajiye gawa na asibitin Sabon Birni dake jihar.

Mutane da yawa da suke zaune a kauyukan sun tattare kayansu sun bar kauyukan saboda tsoron wani sabon harin daga wajen ‘yan bindigar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mohammed Sadiq, ya tabbatar da kai harin ga jaridar Linda Ikeji. Sai dai ya bukaci a bashi lokaci don samo cikakken bayani akan harin.

“Tabbas an kai harin, zan tabbatar da haka gare ku,” ya ce.

Sadiq ya bayyana cewa zai saki rahoto dangane da harin nan ba da dadewa ba.

Haka shi ma tsohon jihar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya wallafa sakon ta’aziyyar shi ga daya daga cikin abokan shi da aka kashe a harin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here