Da duminsa: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 10 a jihar Zamfara

1
407

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sun kai hari kauyen Ruwan Tofa dake karamar hukumar Maru cikin jihar Zamfara, inda suka kashe akalla mutane 10, a rahoton da Daily Trust ta bayar.

Kauyen Ruwan Tofa yana da nisan kilomita 7 da garin Dansadau dake jihar ta Zamfara.

Kamar yadda rahoto ya nuna ‘yan bindigar sun kai hari kauyen sama da shida a cikin wannan shekarar, a cewar wani mazaunin garin mai suna Dahiru Abdullahi.

Mutanen kauyen sun bayyanawa Daily Trust cewa, ‘yan bindigar sun shiga garin da yawan gaske, inda suka zagaye kauyen suka fara harbin mutanen gari akan babura.

“Yan bindigar sun shigo da misalin karfe 5 na yamma a lokacin da yawancin mutanen garin suke gona.

“Sauran mutanen da suka rage a kauyen sun tinkari ‘yan bindigar, amma da yake suna da yawa ‘yan bindigar sunfi karfinsu.

“Sun kashe mutane da yawa a garin, inda kuma suka gudu da dabbobi masu yawan gaske.

“Sun shafe kimanin sa’o’i uku a cikin kauyen kafin su fita.

‘Mutane kimanin 16 da suka ji raunika suna asibitin Dansadau suna karbar magani,” ya kara da cewa.

Sai dai kuma, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya ce wadanda aka kashe duka ‘yan kungiyar sakai ne, kuma suma ‘yan bindigar sun yi musu kwanton bauna ne a lokacin da suke shirin kwato dabbobin da suka sace.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here