Da duminsa: Tsohon manajan NNPC Maikanti Baru ya rasu

0
293

Tsohon manajan kamfanin man fetur na Najeriya NNPC, Maikanti Baru ya rasu.

Shugaban kamfanin na yanzu Mr Mele Kyari shine ya bayyana haka a shafinsa na Twitter.

Ya bayyana cewa tsohon manajan ya rasu a jiya da dare.

Kyari ya bayyana Baru a matsayin dan uwa a gareshi, sannan kuma aboki abin koyi.

“Dan uwana, abokina kuma abin koyi a gare ni, Dr Maikanti Kachalla Baru, tsohon manajan NNPC ya rasu a daren jiya. Babban abin koyi ne kuma abin misali a kasar nan. Allah ya jikanshi da rahama,” Kyari ya bayyana a shafinsa.

An bawa Baru mukamin manajan NNPc a watan Yulin shekarar 2019, inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bashi.

Ya bawa manaja na yanzu Mele Kyari kujerar a shekarar 2019 bayan yayi ritaya sanadiyyar cika shekara 60 a duniya.

An haifi Baru a watan Yulin shekarar 1959, a karamar hukumar Misau dake jihar Bauchi.

Ya halarci makarantar sakandare ta Federal Government College dake Jos, inda ya kammala a shekarar 1978.

A shekarar 1982 ya kammala karatun digirinshi na farko daga jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Sannan yayi digirin digirgir a fannin na’ura mai kwakwalwa a jami’ar Sussex dake kasar Birtaniya.

Shine manajan kamfanin NNPC na 18.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here