Da Duminsa: Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 135 a jihohin Katsina da Zamfara

0
224

Rundunar sojin ‘Operation Hadarin Daji’ ta kai wa ‘yan bindiga dake dajin Katsina da Zamfara a tsakanin ranekun 20 ga watan Mayun nan zuwa 22, inda suka samu nasarar kashe mutum 135.

Manjo Janar John Enenche ne ya bayyana haka a jiya Asabar, inda ya bayyana cewa sojojin kuma sun samu nasarar tarwatsa sansanin ‘yan bindigar a cikin dazuka.

Ya ce sun samu nasarar kai wannan hari ta jiragen sama bayan sun samu wasu bayanan sirri akan wuraren da ‘yan ta’addar suke.

Yace sansanin ‘yan ta’addar sun hada da sansanin Abu Radde da sansanin Dunya dake kananan hukumomin Jibia da Dan Musa dake jihar Katsina, sai kuma sansanin Hassan Tagwaye, sansanin Alhaji Auta da kuma sansanin Maikomi dake kananan hukumomin Birnin Magaji da Zurmi duka a cikin jihar Zamfara.

Enenche ya ce sojojin sun kai wa ‘yan bindigar hari ne ta hanyar jefa musu bama-bamai ta sama, inda suka dinga mutuwa a take a wajen.

Ya ce a ranar 20 ga watan Mayu, a sansanin Abu Radde, yace sun samu nasarar tarwatsa sansanin inda nan ne daya daga cikin manyan shugabannin ‘yan bindigar yake, bayan kashe mutane da dama daga cikin ‘yan bindigar wasu sun gudu da muggan raunika inda suka shiga cikin dajin Dumburum. Ya ce irin wannan harin aka kai sansanin Hassan Tagwaye da Alhaji Auta da kuma Maikomi inda duka aka samu gagarumar nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here