Da Duminsa: Sarkin Musulmai ya amince jama’a su gabatar da sallar idi a Masallatan Juma’a

0
184

Mai girma Sarkin Musulmai, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya lamincewa al’ummar Musulmai ta Najeriya su gabatar da jam’in sallar idi a cikin Masallatan Juma’a.

Fadar Sarkin Musulman ta bayyana hakan, inda ta ce mutane za su iya gabatar da sallar a cikin Masallatan Juma’a ba sai sun fita filin idi ba saboda gujewa yaduwar cutar Coronavirus.

Sanarwar ta fito daga wajen kwamiti dake bawa Sarkin Musulman shawara ta musamman akan harkokin addini, wacce ta fitar a jiya Alhamis.

Sanarwar dai na zuwa ne kwana daya bayan kungiyar Jam’atul Nasril Islam (JNI) wacce ke karkashin shugabancin Sarkin Musulmai, ta fitar da sanarwar cewa kowa ya gabatar da sallar idi a cikin gidansa tare da iyalansa.

Idan ba a manta ba a ko a rahoton da Press Lives ta kawo muku jiya fadar mai girma Sarkin Musulmin ta bayyana cewa sai dai idan har ya zama dole sai an gabatar da jam’i, musamman a wasu jihohi da aka bayar da damar gabatar da sallar a cikin jam’i.

Wannan sabuwar sanarwar ta biyu da BBC ta ruwaito ta bayyana cewa fadar ta ce: “An bukaci dukkanin manyan kasa, sarakuna, hakimai, limamai dasu gudanar da sallolin idi a cikin masallatan Juma’a a garuruwansu ba tare da kowa ya fita filin idi ba.”

A karshe dai fadar Sarkin Musulman ta yi kira ga al’ummar Musulmai ta kasa baki daya akan su dage da addu’o’i na neman Allah ya kawo karshen wannan annoba.

Tuni gwamnonin jihohin irinsu, Kano, Yobe, Borno, Bauchi, Zamfara, Jigawa da sauransu suka bawa al’umma damar fita su gabatar da sallar idi a jam’i.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here