Da duminsa: Mataimakin gwamnan Bauchi ya kamu da cutar Coronavirus

0
378

Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Sanata Baba tela, ya kamu da cutar coronavirus.

Tela shine shugaban kwamitin gudanarwa na cutar ta COVID-19 ta jihar.

A wata sanarwa dauke da sa hannun babban mai taimakawa gwamnan jihar a fannin sadarwa, Mukhtar Gidado, ta ce an gano cewar yana dauke da cutar ne bayan gabatar da gwaji da aka yi a jikin shi, bayan fara ganin alamun cutar a jikinshi.

“Ya dauki cutar ne a lokacin da yake aiki tukuru a matsayin shi na shugaban kwamitin gudanarwar,” cewar Gidado.

Sanarwar ta bayyana cewa tuni an killace mataimakin gwamnan jihar inda ma’aikatan lafiya suke lura da shi.

“An dauki samfurin duka mutanen da ya hadu da su, kuma an bukaci su killace kansu kafin sakamakon gwajin ya fito,” cewar sanarwar.

Haka kuma gwamnan jihar Bala Mohammed, wanda shi ma ya sha fama da cutar a kwanakin baya, na taya mataimakin gwamnan addu’a akan samun lafiya cikin gaggawa.

Gwamnan yayi kira ga duka mutanen jihar da su bi dokokin da aka gindaya akan wannan cutar don rage yaduwar ta a cikin al’umma.

A jiya ne dai gwamnatin tarayya ta cire dokar hana zuwa wuraren ibada a fadin Najeriya.

Gwamnatin ta cire dokar ne a bisa sharadin cewa kowa zai bi dokokin da hukumomin lafiya da gwamnatocin jihohi suka gindaya.

Haka kuma a safiyar yau dinnan Press Lives ta ruwaito muku cewa gwamnatin tarayyar ta bayar da umarni a kowanne masallaci da coci a dinga daukar sunayen wadanda suke zuwa ibadan don samun sauki wajen bin diddigi koda cutar ta barke.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here