Da duminsa: Iya ‘yan kasar Saudiyya ne kawai za su yi aikin Hajjin bana – Gwamnatin Saudiyya

0
287

Gwamnatin kasar Saudiyya ta bayyana cewa aikin Hajji na wannan shekarar da za ayi a wata mai zuwa, iya mutane kalilan ne za a bari su samu halarta.

Ta kuma ce wadanda za su halarci aikin Hajjin za su zamo daga kasashe daban-daban, amma kuma iya wadanda ke zaune a cikin kasar a yanzu.

Ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta kasar ta bayyana haka a ranar Litinin, inda ta ce ta dauki wannan mataki ne saboda annobar coronavirus da ake fama da ita.

Ma’aikatar ta ce ta yanke shawarar hakan ne bisa la’akari da ganin har yanzu cutar na cigaba da yaduwa cikin al’umma, kuma tana iya kamari a wajen da mutane suka taru da yawa.

“Iya mutane kalilan ne wadanda suke zaune a kasar Saudiyya za a bari suyi aikin Hajji.

“Mun yanke wannan shawara ne don tabbatar da cewa anyi aikin Hajji lafiya an gama lafiya ta hanyar bin duka dokokin da suka dace,” cewar ma’aikatar ta aikin Hajji da Umrah.

A shekarar da ta gabata mutane miliyan 2.5 ne dai suka gabatar da aikin Hajji a kasar ta Saudiyya.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here