Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta rage kudin aure a Najeriya

1
8935

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta rage kudin gudanar da aure a Najeriya. Sabon kudin da ta sanya zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Yuli.

Sabon kudin ya zo karkashin dokar aure ta CAP M6 LFN 2004, a cewar sanarwar da babban sakatare kuma mai rijistar aure a Najeriya, Georgina Ehuriah.

Wata sanarwa daga daraktan yada labarai na ma’aikatar cikin gida ta Najeriya, Mohammed Manga, ta bayyana cewa hakan wani garambawul ne da gwamnati za tayi a fannin auren bayan samun shawarwari daga masu ruwa da tsaki a kwanan nan.

Lasisin yin aure a wuraren bauta an rage shi daga N30,000 na tsawon shekara biyu zuwa N6,000 a kowacce shekara.

Sabunta lasisin auren a wajen bauta, an amince a dinga biyan N5,000 a kowacce na tsawon shekara uku. Yayin da a da yake N30,000 kowacce shekara.

Hakanan an rage kudin daurin aure daga N21,000 zuwa N15,000, inda aka rage kudin lasisi na musamman daga N35,000 zuwa N25,000.

A kwanakin baya mun kawo muku rahoton fitacciyar jarumar fina-finan kudancin Najeriya na Nollywood, wacce ta bukaci a daina biyan kudin aure baki daya.

Toni Tones dai ta ce mata ba kadarori bane da za a ce duk lokacin da za ayi aure sai an biya musu sadaki ba. Ga dai cikakken labarin: Kamata yayi a haramta bayar da sadaki ga mata a lokacin aure – Toni Tones

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here