Gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar, ya hana bikin sallah babba da kuma hawan sallah da aka saba yi kowacce shekara a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakane a jiya Talata 21 ga watan Yuli a lokacin da yake magana da manema labarai a garin Dutse babban birnin jihar.

Ya ce ya yanke hukuncin ne a kokarin da jihar take yi na yaki da cutar coronavirus.

A cewar shi, jihar Jigawa tuni ta samu nasara a yaki da wannan annoba mai kisa, inda yace akwai bukatar a cigaba da kokari wajen hana yaduwar cutar a jihar.

“Duk da wannan cigaba da aka samu, jihar za ta cigaba da kokari wajen yaki da cutar domin hana yaduwar cutar da kuma kawo cigaba wajen yaki da annobar,” cewar gwamna Badaru.

Ya sake bayar da bayani dangane da wannan lamari a wata hira da yayi da ma’aikacin jaridar gidan gwamnatin jihar, inda ya ce;

“Mutum daya ne kawai ya rage a wajen duba masu cutar coronavirus. Wadanda suke Fanisau da Birnin Kudu tuni an kulle su, amma kuma an ajiye su cikin tsafta koda wani abu na bukatar su zai ta so.”

Gwamnan ya kara da cewa kasuwanni a fadin jihar tuni suna bin dokokin da hukumomin lafiya suka gindaya, hakan ya sanya aka bari suka cigaba da kasuwanci.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here