Wani rahoto da jaridun kasar Saudiyya suke ruwaitowa ya nuna cewa an kwantar da Sarkin kasar ta Saudiyya, Salman bin Abdulaziz sakamakon fama da kumburi da yake yi a mafitsararsa.

Sarkin mai shekaru 84, wanda yake kan kujerar mulkin kasar tun shekarar 2015, yanzu haka dai yana kwance ana duba lafiyarsa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar (SPA), ya ruwaito a jiya Litinin, 20 ga watan Yuli, sai dai basu bayar da karin bayani ba.

Firaministan kasar Iraqi Mustafa Al-Kadhimi ya daga zuwa ziyarar da zai kai birnin Riyadh sakamakon rashin lafiyar Sarkin, cewar ministan kasashen waje na kasar ta Saudiyya.

“Sakamakon duba da muka yi dangane da muhimmancin ziyarar da kuma son ganin komai ya tafi yadda ya kamata, shugabannin mu tare da hadin guiwar ‘yan uwanmu na kasar Iraqi sun yanke shawarar daga ziyarar,” Yarima Faisal bin Farhan Al Saud ya rubuta a shafinsa na Twitter.

Idan ba a manta ba mun kawo muku rahoton cewa kasar ta Saudiyya ta dauki mata aiki a manyan Masallatan kasar guda biyu na Ka’aba dake garin Makkah da kuma Masallacin Annabi dake birnin Madina.

An dauki matan aiki ne domin su dinga kula da kuma gyara bangaren mata na cikin Masallatan, don tabbatar da tsaro da kuma lafiyan masallata kamar yadda hukumomin lafiya na kasar suka gindaya, don dakile yaduwar cutar coronavirus a kasar.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here