Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 15 a Katsina

0
287

Mutane goma sha biyar sun mutu sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen ‘Yar Gamji dake karamar hukumar Batsari cikin jihar Katsina, a jiya Litinin 6 ga watan Yuli.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, shine ya tabbatar da kai harin, inba ya ce, ‘yan bindigar sun shiga garin kimanin su 200, akan babura, inda suka kai harin da misalin karfe 10:00 na safe suka yi ta harbin jama’a, hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutum 15.

A cewar Isah, jami’an tsaron dake yankin sun hada runduna, sun kai wa ‘yan bindigar hari kafin su kashe wasu mutane, inda ‘yan bindigar suka gudu.

A ‘yan kwanakin nan dai jihar ta Katsina na ta samun hare-hare na ‘yan bindiga a lokuta da dama, duk da kokarin da gwamnati ta ce tana yi wajen kawo karshen lamarin.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here