Da biskit nake yaudarar yara na yanka su na sayar da sassan jikin su – Cewar wani saurayi

0
2498

Rundunar shige da fice ta kasa reshen jihar Oyo ta kama wani saurayi dan shekara 29 da laifin garkuwa da kuma kashe yara.

Saurayin wanda ba a bayyana sunanshi ba mazaunin Beere ne dake yankin Oje cikin garin Ibadan, yana daya daga cikin ‘yan kungiya su tara da suka hada da mata guda biyu da kuma maza guda bakwai da suke wannan aika-aika.

Jami’an tsaron sun kama shi, bayan wani dan acaba ya sanar da su game da hannun mutumin a satar yara da kuma sayar da sassan jikinsu ga matsafa.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Olufemi Adetunji, ya bayyana haka ga manema labarai a jiya Juma’a, a yayin da suke mika mai laifin ga rundunar ‘yan sandan jihar.

Saurayin ya amsa laifinsa bayan hira da yayi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), inda ya ce ya kashe akalla yara guda biyu, sannan ya sayar da sassan jikinsu ga matsafa.

Ya bayyana cewa shi da abokanan aikinsa suna yaudarar yara da biskit ne, sai su jawo su zuwa cikin mota. Ya ce.

“Muna da mota da muke satar yara da ita. Muna sayen biskit da sauran abubuwa mu sanya a cikin motar, inda muke amfani da su mu yaudaro yaran cikin motar.

“Duk lokacin da muka ga yaro yana tafiya a titi shi daya ba tare da wani babba ba, sai mu ce zamu basu biskit da sun zo sai mu rufe mota mu gudu.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here