Da ba dan addu’ar da muke yi ba da tuni Najeriya ta tarwatse – Martanin Sakataren Tarayya akan Coronavirus

0
151
President Muhammadu Buhari in a handshake with the SGF Mr. Boss Mustapha during an audience with Founder of Dana Air the State House, Abuja. PHOTO; SUNDAY AGHAEZE. JULY 3 2019.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana cewa addu’a ce ta saka har yanzu annobar Coronavirus ba ta tarwatsa Najeriya ba.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake magana a dakin majalisar wakilai a jiya Talata 5 ga watan Mayu, Mustapha wanda yake jagorantar kwamitin kula da annobar ta Coronavirus ya ce, “da tuni Najeriya ta tarwatse da ba dan addu’a da muke ba.”

Sakataren yaje dakin majalisar wakilan tare da wasu daga cikin ‘yan kwamitin kula da cutar ta Coronavirus domin yiwa ‘yan majalisar bayani akan halin da ake ciki dangane da kokarin su na cigaba da yaki da cutar.

Yace a yayin da kasar take cigaba da samun cigaba wajen yaki da cutar, “addu’a na daya daga cikin abinda ta taimakawa Najeriya take inda take a yanzu.”

“Addua’a ce ta taimaka har muka kawo wannan matsayin a Najeriya. Na tabbata addu’a na da matukar tasiri, sannan kuma zamu gana da sarakunan gargajiya da malaman addini akan wanna matsalar,” ya ce.

“Hatta a cikin wannan wata na Ramadana, mutane na ta addu’a, suna rokon Allah ya kawo karshen wannan annobar kuma ya kare kasar mu dama duniya baki daya.

“A yanayin yadda muke gani kasashen duniya na fama da cutar, ya zuwa yanzu yaci ace Najeriya ta tarwatse, amma saboda tasirin addu’a yasa har yanzu lamarin bai fi karfin mu ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here