Cutar Korona gaskiya ce domin ko ni kaina na san wanda yake dauke da cutar – Dino Melaye

0
586

Tsohon sanatan jihar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye ya tabbatar da gwaje-gwajen da hukumomin lafiya suke yi, inda ya tabbatar da cewa akwai cutar a jihar ta Kogi.

Idan ba a manta ba gwamnatin jihar Kogi taki amincewa da batun samun mutane biyu da cibiyar binciken manyan cututtuka ta Najeriya tayi da suka kamu da cutar a jihar a ranar Laraba 27 ga watan Mayun nan.

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar 30 ga watan Mayu, tsohon sanatan ya ce tabbas gwajin da aka yi a jihar gaskiya ne saboda shi kanshi ya san wani daga karamar hukumar Kabba da yake dauke da cutar.

Dino Melaye ya ce:

“Ina so na sanar da cewar cutar korona a jihar Kogi gaskiya ce, amma ban san mai yasa gwamnati take musanta bullowar cutar ba saboda kawai tana so ta kashe mutanen jihar.

“Daya daga cikin masu cutar dan karamar hukumar Kabba ne, kuma ni kaina na san shi. Ba zan zama daga cikin wadanda zasu yi wasa da rayukan al’ummar jihar nan ba.

“COVID-19 gaskiya ce, amma ba wai hakan na nufin mutuwa ce ba, idan har an dauki matakin da ya dace. ‘Yan uwan mutumin da ya kamu da cutar a Kabba da sauran wadanda suka yi mu’amala da shi su kai kansu domin ayi musu gwaji, don dakile yaduwar cutar.

“Gwamnatin jihar Kogi ta shiga taitayinta ta fara neman mutanen da suka hadu da wannan mutumin don dakile yaduwar cutar a jihar. Rashin tunani ne ayi tunanin ba zamu samu cutar ba bayan duk jihohin da suka zagaye mu akwai ta.

“Allah zai amsa addu’ar mu ya cire cutar daga kasar mu. Allah ya taimaki jihar Kogi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here