COVID-19: Za a fara bi gida-gida ana gwada mutane a jihar Kano – Ganduje

0
395

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da umarnin bin gida-gida domin gwada mutanen da ake zargin suna dauke da cutar coronavirus a cikin kwaryar birnin Kano.

Gwamnan ya bayyana hakane a jiya Alhamis, bayan sanarwar da kwamitin gudanarwa ta COVID-19 ta bayar na cewa cutar na cigaba da yaduwa sosai a cikin kwaryar birnin Kano.

Da yake magana a lokacin taron da kwamitin ta gudanar a gidan gwamnatin jihar, gwamnan ya ce: “zamu fara bi gida-gida don gwada mutane.”

“Ina tunanin lokacin yakin neman zabe wasu ‘yan siyasar sun bi gida-gida wajen gabatar da kamfen.

“Saboda haka a yanzu haka zamu dinga bi gida-gida don gwada mutane, kuma zamu gabatar da gwajin a cikin kananan hukumomi guda takwas dake cikin fadin kwaryar Kano.

Gwamnan ya bayyana cewa jihar na cigaba da samun nasara a yaki da cutar ta coronavirus a fadin jihar, inda ya kara da cewa dokoki guda uku na wanke hannu, sanya takunkumi da kuma dokar nisantar juna dole su zama daya daga cikin abubuwan da mutane za suke gabatarwa yau da kullum.

Tun a farko, a nasa jawabin, babban jami’in kwamitin gudanarwa na jihar, Dr. Tijjani Hussaini, ya ce daga cikin mutane 970 da aka samu a jihar, yanzu haka mutane 607 ne kawai suka rage, inda mutum 318 suka warke aka kuma sallame su daga asibiti.

A cewar shi, yawancin wadanda ake samu dauke da cutar suna fitowa daga kananan hukumomi guda tara na cikin kwaryar birnin Kano ne.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here