Coronavirus ta tona asirin azzaluman shugabanni a Najeriya – Sheikh Gumi

0
204

Fitaccen Malamin addinin Musuluncin, Sheikh Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, yayi gargadi akan wasa da rayukan al’ummar Najeriya da shugabanni suke yi.

A Tafsirin da ya gabatar a ranar Juma’a wanda Mustapha Yamusa Rigasa ya nada a shafin Facebook, ya ce gwamnoni da suke gaggawar cire dokar hana zirga-zirga a jihohinsu, ba wai suna yi domin coronavirus ba gaskiya bace, yace suna yi ne saboda sun tabbatar da cewa baza su iya tafiyar da jihohinsu ba a lokaci irin wannan.

Wannan magana tashi ta zo ne bayan rahoton da aka fitar na cewa wasu gwamnoni musamman daga yankin arewa za su cire dokar hana fita da suka sanya a jihohinsu duk kuwa da kara samun masu cutar Coronavirus da ake yi a yankin.

Malamin ya ce gwamnonin suna da ikon kyale mutane su fita suyi siyayya a kasuwa domin su ajiye kayan abinci. Ya ce zuwa kasuwa ya zama tilas ga al’umma tunda gwamnonin sun kasa rabawa mutane kayan tallafi, bayan kulle su da aka yi a cikin gida tun a cikin watan Maris.

Haka kuma, Gumi ya kara da cewa bai kamata a bar mutane su dinga taruwa ba musamman a Masallatai da coci domin ibada.

Ya ce: “Amfani da wuraren bauta wajen cire dokar hana zirga-zirga ba abu bane mai kyau. Wannan bai kamata ba gwamnoni su dinga amfani da Masallatai wajen cire dokokinsu, saboda Musulunci bai yadda mutane su dinga zuwa Masallaci ba lokacin annoba. Kowa zai iya sallah a gida a lokacin da ake fama da annoba.

“Kuna sanya mutane cikin hadari, zaku iya kyale mutane suje su sayo kayan abinci, amma ku cire Masallaci a cikin dalilin cire dokokin ku,” cewar Dr Gumi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here