Coronavirus ta saka mu cikin tashin hankali, yunwa na neman kashe mu – Karuwan Najeriya sun koka

0
721

A wata hira da wani dan jarida da ya bukaci a sakaye sunanshi yayi da wata karuwa, yayi mata tambayoyi akan yadda rayuwarsu take a wannan lokacin na coronavirus.

A lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da sanarwar cewa zai hana zirga-zirga a jihohin Lagos, Ogun da Abuja, a kokarin dakile yaduwar cutar coronavirus da yake yi a Najeriya, mutane suna ta tunanin yadda masu kananan sana’a za su yi a wannan lokaci.

Idan aka yi maganar kananan masana’antu mutane na tunanin kananan shaguna dake bisa titi, da wuraren sayar da abinci, da masu kosai da sauransu.

Amma ta wani bangaren hatta karuwai suma suna cikin jerin masu kananan sana’o’i, da irin wannan ne nayi tunanin tambayar daya daga cikin yammatana da na gani da dare akan yadda kasuwancinsu yake tafiya a wannan lokaci na coronavirus.

Cikin sa’a na samu wata daga cikinsu wacce muka boye sunanta don kare ta, ta nuna cewa a shirye take ta amsa tambayoyina, ta bayyana yadda rayuwa ta canja musu a wannan lokaci, haka kuma ta bayyana dalilin da ya sanya ta shiga karuwanci da kuma nawa take samu a kowacce rana da wannan sana’a.

Kin ce ke karuwa ce amma mai aji, mai kike nufi da haka?

“Abinda ya sa na zama daban da sauran shine, ni bana zuwa na dinga neman otel, Akan titi nake harka ta. Namiji zai dauke ni yayi amfani dani, idan ya gama ya biyani. Haka muke yi.

Idan mutum yana so ya fara wannan sana’ar daga yaya zai fara?

“Ba wani abu bane mai wahala, mutum zai yi wanka ne kawai, ya sanya kaya masu kyau ya tsaya a bikin titi. A duk inda kaga mace a tsaye a bakin titi a tsaye mutum yaje ya tsaya, idan kayi tsautsayi ka shiga hannun ‘yan sanda labari ya sha banban?

Nawa kike samu a kowacce rana?

‘Idan Allah ya taimakeka zaka samu kudi sosai, wani lokacin ina samun N10,000, idan na fito da misalin karfe 8 zuwa 9. A sati kuma ina samun dubu 35,000 dubu 40,000 wani lokacin ma har 45,000. A wata kuma ina samun 100,000 wani lokacin. Matsalar ita ce yadda kudin yake zuwa haka yake tafiya kamar ruwa.

Mene yasa kika shiga wannan harkar?

“Yanayin rayuwa ce, Ina zuwa makarantar sakandare, amma ina zuwa kamar jami’a ne. Ina neman kudin saboda ina so naje jami’a saboda haka idan na samu kamar dubu 400 zan daina wannan harkar.

Yanzu kina ganin Allah zai albarkace ki da wannan sana’ar?

‘Na san irin wannan aikin haramun ne, amma na san Allah yana amsa addu’a ta. Idan har baya amsa addu’a ta da tuni na fada hannun ‘yan kungiyar asiri. Allah ne kawai yake kare mu.

Ya wannan dokar hana zirga-zirgar take shafar sana’arku?

“Wannan dokar na damun mu matuka, duka otel din da muke zuwa basa budewa yanzu. Yunwa na neman kashe mu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here