Coronavirus: Shugaba Buhari zai gabatar da sallar idi a gida tare da iyalansa

1
271

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da sallar idi a gida tare da iyalansa.

Karamar salla dai sallah ce da aka saba gabatarwa a karshen kowanne watan Ramadana. Bayan sallar kuma ana gabatar da bukukuwa don murnar zuwan karshen watan Ramadana.

Wannan shekarar ana sa rana za a gabatar da sallar tsakanin ranar Asabar da Lahadi a kasashen duniya.

Kamar kowacce kasa dai Najeriya ta sanya dokar hana zirga-zirga da kuma gabatar da taro da ya kunshi mutane da yawa domin dakile yaduwar cutar ta Coronavirus.

Ga dai sanarwar fadar shugaban kasar akan yadda shugaban kasar zai gabatar da sallar idin a wannan shekarar.

“A yayin da bikin karamar sallah yake karatowa, kuma watan Ramadana yake shirin wucewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da sallar idin shi a gida tare da iyalansa.

“Wannan dai na zuwa ne bayan dokar da aka sanya a babban birnin tarayya Abuja, domin kare rayukan al’umma daga wannan cuta.

“Haka kuma na da nasaba da umarnin da mai girma Sarkin Musulmi, kuma shugaban kungiyar Jama’atul Nasril Islam, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya bayar ta dakatar da sallar idi a jam’i a fadin Najeriya.

“Domin kuma bin dokar da gabatar da taron mutane da yawa kamar yadda kwamitin sanya ido akan cutar ta Coronavirus ta saka.

“Bayan haka shugaban kasar da ya saba gabatar da bikin sallah tare da manyan jami’an gwamnati, manyan ‘yan siyasa, shugabannin al’umma, shugabannin addinin Musulunci dana Kirista da kuma yara, a wannan karon ba zai karbi bakuntar kowa ba a kokarin dakile yaduwar cutar a cikin al’umma.”

Garba Shehu

Babban mai bawa shugaban kasa shawara ta musamman

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here