Buhari zai yi babban kuskure idan har ya cire dokar hana zirga-zirga a Najeriya – Sheikh Ahmad Gumi

0
148

Fitaccen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce babban kuskurene idan har shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cire dokar hana zirga-zirga a Najeriya, yayin da kasar take fama da wannan masifa ta annobar Coronavirus.

A ranar 27 ga watan Afrilu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana kudurinsa na cire dokar a jihohin Legas, Ogun, da babban birnin tarayya Abuja.

A wata hira da yayi da New Telegraph, Sheikh Gumi ya ce gwamnatin tarayya kada ta kuskura ta cire dokar ga ‘yan Najeriya, amma ta nemi wata hanya ta hana yaduwar cutar ga al’umma.

Ya bayyana cewa gwamnati na neman watsi da lamuran jama’a ne shine yasa take so ta cire dokar, ya kara da cewa mutane na kulle a gidaje cikin yunwa, kuma gwamnati ba ta shirya tallafa musu ba.

“Gwamnati na shirin watsi da jama’a ne shine yasa take son cire dokar, wannan shine gaskiyar magana, mutane na kulle a gidaje cikin yunwa kuma gwamnati ba ta shirya tallafa musu ba. shine yasa suke ganin hanyar da tafi dacewa shine su cire dokar, wannan babban kuskurene.

“Hatta kasar China da suka cire dokar hana fita, sun sanya doka a makarantunsu kowanne dalibi sai yaje da takunkumin fuska, sai an gwada yanayin mutum kafin a barshi ya shiga aji. Shin zamu iya yin irin haka a nan? Ba zamu iya ba.”

Ya cigaba da cewa: “Gaskiyar magana ban ma san irin kalmomin da zanyi amfani da su wajen bayyana abinda ke faruwa ba, tsakanin gwamnatin da kuma al’umma. Amma bari nayi magana akan gwamnati tunda ita ta riga ta san abinda ya kamata tayi. Gwamnati tana kokarin janye kanta saboda sakota a gaba da aka yi, amma yawan da muke da shi ma wani abu ne.

“Mutane sun zama tamkar yara, kana kokarin kayi musu abinda yafi dacewa dasu, amma su kuma sunki bada hadin kai. Amma ta wani bangaren banga laifinsu ba, saboda suna cikin yunwa, an barsu babu ilimi, ba a koyar dasu halin da ake ciki ba, hatta Malaman addini sunki su gaya musu gaskiyar abinda ke faruwa. Hatta wasu da suke nuna cewar basu yadda da cutar ba sun dauka daga wajen Malaman su ne. Amma gwamnati ba ta abinda ya dace gaskiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here