Buhari yaki yiwa ‘yan Najeriya bayani ne saboda gudun mutanen da zasu ci mishi mutunci – Shehu Sani

0
192

Tsohon dan majalisa mai wakilatar jihar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya bayyana dalilin da ya saka shugaba Buhari yaki yadda ya yiwa ‘yan Najeriya bayani a jiya Litinin.

A ranar Lahadi ne shugaban masu shirye-shirye na kwamitin kula da cutar Coronavirus ta Najeriya, Aliyu Sani ya bayyana cewa Buhari zai yiwa ‘yan Najeriya bayani a jiya Litinin da yamma.

Sai dai kuma, a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya sanar da cewa shugaban kasar ba zai yi bayani ba a jiya Litinin din.

Da yake mayar da martani akan wannan bayani a shafinsa na Twitter, Shehu Sani ya bayyana cewa shugaba Buhari yaki yadda yayi bayanin ne saboda gudun maganganun ‘yan Najeriya na cin mutunci.

“Baba Buhari ya so ya fito yayi muku bayani, amma lokacin da ya leko ta taga maimakon yaganku rike da litattafai sai ya ganku rike da duwatsu. Hakan ya tilasta shi komawa daki, ku mayar da duwatsunku daga inda kuka dauko su,” inji Shehu Sani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here