Buhari yafi yarda da mata fiye da maza a gwamnatinsa – Garba Shehu

1
408

Babban mai bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a fannin sadarwa, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa shugaban kasar yafi yadda da mata a gwamnatinsa fiye da maza.

Mai magana da yawun shugaban kasar ya bayyana haka ne a lokacin da yake hira da NTA a ranar 29 ga watan Mayu. Da aka tambayeshi ko shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bawa mata mukami, Shehu ya ce;

“Wannan addu’a ce kuke yi nima kuma ina fata. Ina ganin zai fi ya saka mata da yawa a cikin gwamnatinsa.

“Banda haka kun san cewa duka ministocinsa na kudi duka mata ne?

“Bari na ce wani abu, ina fatan bazan sanya kai na cikin matsala ba. Ina ganin yafi yarda da mata fiye da maza, saboda duk shekarun da yayi yana mulki duka kudin kasar yana hannun mata ne, kuma sun ajiye kudin ba tare da matsala ba. Suna kokari kuma sosai.”

A bangaren yadda shugaban kasar yake tafiyar da rayuwar shi a lokacin da bashi da aiki, Garba Shehu ya ce shugaban kasar yana zama da jikokin shi a lokacin da bashi da aikin yi, kuma yana dan yin tattaki cikin gida ko a waje don motsa jini.

Ya kara da cewa;

“Shugaban kasar kuma yana kallon talabijin, yana kallon shirin namun daji, sannan yana daukar lokaci mai tsawo yana kallon NTA.

“Yana son wasa da jikokinshi, yana da jikoki da yawa kuma yana jin dadin wasa tare da su a koda yaushe.

“Yana tattaki a cikin gida ko a waje, don motsa jinin jikinshi.”

Ya zuwa yanzu dai mata bakwai ne kawai a cikin ministoci arba’in da uku da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake da su a Najeriya.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here