Buhari ya saka a karbo maganin Coronavirus daga kasar Madagascar

0
110

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci a karbo maganin Coronavirus daga kasar Madagascar, shugaban kwamitin masu kula da cutar ta Coronavirus dake Najeriya, Boss Mustapha, shine ya bayyana haka a jiya Litinin.

Da yake magana da manema labarai jiya a Abuja, Sakataren Gwamnatin Tarayyar ya ce, sai an gabatar da kwakkwaran bincike akan maganin kafin a bari mutane su fara amfani da maganin a Najeriya.

“Shugaban kasa ya bani umarnin a shigo da maganin Najeriya, kuma ya wakilta ni na lura da yadda za a gabatar da bincike akan maganin, sai an tabbatar da sahihancin sa kafin a bari mutane su fara amfani da shi.” Cewar shi.

Haka shi ma da yake magana a wajen taron, ministan lafiya, Dr. Osagie Ehanire, ya ce za a gabatar da bincike akan maganin a cibiyar binciken magunguna ta Najeriya, domin tabbatar da sahihancinsa kafin a bari al’umma su fara amfani da shi.

“Za mu karbo maganin daga kasar mu gabatar da gwaji a kai, sannan zamu yi magana da hukumominsu na lafiya domin suyi mana bayani akan yadda suka yi amfani da maganin.

“Haka kuma zamu bawa kwamitin binciken magunguna ta kasar nan domin su gabatar da nasu binciken domin ganin abinda ya kamata ayi akan maganin.

“Mun gano cewa wata itaciya ce mai suna Artemisia Annua, wacce muna da ita muma a nan. Amma muna so muga irin tasu domin mu hada ta da tamu mu gani ko iri daya ce.

“Duka kasashen duniya suna iya bakin kokarinsu wajen gano maganin cutar, saboda haka bamu da banbanci da su, zamu yi iya bakin kokarinmu wajen ganin muma mun tabuka wani abu.

“Kafin mu fara bawa mutane wannan maganin sai mun tabbatar da cewa bashi da wata matsala, sannan kuma sai mun tabbatar da cewa yana aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here