Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya bayyana dangantakar dake tsakaninsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin ta uba da da, duk da ya koma jam’iyyar PDP.

Obaseki ya bayyana hakane a shafinsa na Twitter, yayin da ya bayyana cewa yana ganawa da shugaban kasar a manhajar Zoom.

A cewar Obaseki: “Dangantakar dake tsakanina da shugaban kasa Muhammadu Buhari, tamkar ta da da mahaifi ce. Na gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a manhajar Zoom, inda muka yi magana dangane da matsalolin dake damun jihar Ondo dama Najeriya baki daya.

“Haka kuma munyi magana akan hanyoyin da zamu bi domin dakile yaduwar cutar COVID-19.

Obaseki dai ya bar babbar jam’iyyar APC mai mulki ya koma jam’iyyar adawa ta PDP a yayin da ake shirin gabatar da zaben gwamnan jihar.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here