Budurwa ta yi karyar ta mutu a Facebook saboda tana so mahaifiyarta ta daina tambayar ta kudi

0
493

Wata budurwa ‘yar shekara 19 mai suna Margaret Adiya Ikumu, wacce ke zaune a jihar Legas, ta bayyana yadda tayi karyar ta mutu a shafin sada zumunta saboda tana so ta daukewa kanta nauyin wahala da mahaifiyarta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Bala Elkana, ya ce labarin mutuwar budurwar anyi ta wallafa shi a shafukan sada zumunta inda har ya kai ga iyayenta.

A wata sanarwa da aka fitar a ranar 24 ga watan Mayu, Bala yace a ranar 15 ga watan Mayu sun samu takarda daga wajen wani mai suna Tony Iji, da sunan iyayen Margaret, inda suka bayyana cewa hankalinsu ya zo kan wani rubutu da aka wallafa a shafin Facebook inda aka bayyana cewa Margaret ta mutu kwanaki kadan da suka wuce, kuma wasu abokananta guda biyu masu suna Marvelous Mary da Nneka Buddy sun binne ta a Ajah.

Haka iyayen yarinyar sun bayyana cewa sun tuntubi kawayen nata inda suka tabbatar musu da cewa tabbas ta mutu.

Bayan bincike da aka gabatar, ‘yan sanda sun gano cewa Margaret na nan da ranta, kuma tayi karyar ta mutu ne saboda ta saukewa kanta wahalar kashe kudin da take yiwa mahaifiyarta.

“Sun bayyanawa ‘yan sanda cewa kawayen ta sun sanar da su cewa ta basu umarnin kada su bari ‘yan uwanta su san komai dangane da mutuwarta, sannan kuma suka bayyana cewa ita ce ta basu wasiyyar su binne ta a boye. Don su tabbatar da cewa ta mutu, har hotuna suka aikawa daya daga cikin ‘yan uwan Margaret a WhatsApp na akwatin gawa. Haka kuma an kashe wayar yarinyar baki daya. Haka kuma iyayenta sunyi magana da wani mutumi da ya bayyana cewa shine saurayinta. Shi ma ya kara tabbatar musu da cewa ta mutu.” cewar sanarwar.

Margaret wacce ‘yar aiki ce a wani gida dake Ajah, wadanda suka dauke ta aiki sun kai kararta ga ‘yan sanda. A cewar ‘yan sandan, tayi fushi da iyayenta ne saboda sun kasa daukar nauyinta tayi karatu.

“Bayan mutanen da take aiki a gidansu sun ga wannan rubutu na cewa ta mutu a shafin Facebook, sai suka yi gaggawar sanar da ‘yan sanda inda aka kai ta ofishin ‘yan sanda na Ajah. Ta sanar da cewa ta tayi karyar ta mutu ne saboda iyayenta su rabu da ita. Ta ce mahaifiyarta tana damunta da matsalar kudi a koda yaushe. Yarinyar tana fushi da mahaifiyarta da kawunnin ta akan sun kasa daukar nauyinta tayi karatu bayan rasuwar mahaifinta. Abinda ya kai ta Legas shine tayi aiki ta samu kudi ta koma makaranta.

“Ta bayyana cewa tayi amfani da hoton ‘yar gidan da take yi musu aiki a Facebook, inda ta wallafa rubutun mutuwar tan, kawunta ya dauki wannan hoto yayi kira ga jama’a da duk wanda ya san wannan budurwa da ya taimaka ya sanar a ofishin ‘yan sanda mafi kusa,” cewar sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here