Budurwa ta tona asirin Lakcaran da ya nemi yasa ta maimaita shekara daya a jami’a saboda taki amincewa yayi zina da ita

0
314

Wata budurwa ‘yar Najeriya ta bayyana halin da ta shiga a lokacin da malaminsu na jami’a ya dinga yi mata barazanar kayar da ita jarrabawarshi matukar ba ta je ta same shi a dakin otel ba.

A cewar budurwar mai suna @_Faves a shafin Twitter, malamin yayi mata barazanar cewa zai tabbatar da cewa ta maimaita shekara daya a jami’a matukar taki yadda yayi amfani da ita a otel din.

Wata budurwa ta kara da cewa ya kara yi mata wannan barazana a ranar jarrabawarsu, inda ta ce a karshe malamin yaki bata makin jarrabawa, inda aka dakatar dashi aka bawa wani mukaminshi a jami’ar.

Ta ce:

“Ba zan taba manta ranar da lakcara yayi mini barazanar kayar dani jarrabawa ba idan naki yarda na same shi a otel. Naji tsoro matuka a wannan lokacin, sai na shirya da kanwata akan ta saita wayata ta dauki sautin muryar abinda zai faru tsakanina da shi.

“Da naje kofar otel din, sai yace ba wai ina so nayi iskanci dake bane, amma ina so ki zama uwar ‘ya’yana. Ina matukar son yanayin jikinki. Kina matukar bukatar wanda zai kula dake, haka yasa nake ganin bayan kin kammala jami’a sai muyi aure, har ya fara tunanin aurena ni ban sani ba.

“Sai ya ce na zauna, na zauna akan kujera, yazo ya zauna kusa dani ya kama hannuna. Duk wannan lokacin yana magana kasa-kasa, ban san mai yasa ba. Daga baya sai ya tambayeni ina wayata take, nace masa tana cikin jaka. Sai ya dauki jakar ya boye.

“Hakan na nuni da cewa ba wannan ne lokacin da ya fara ba. Sai ya fara taba jikina, ni kuma kayan dana saka ko fyade zai yi mini sai ya sha wahala. Ku duba fa mutumin da yace ba iskanci zai yi dani ba shine yake cewa na cire kayana yana son yaga yanayin jikina, ai kuwa jikina sai ya fara rawa.

“Sai nace masa yayi hakuri ba zan iya ba, abinda ya fito daga bakin shi shine, ina ganin idan kika maimaita shekara daya zaki canja ra’ayi.” Sai na ce masa ba zan iya komai ba idan har ba wai a buge nake ba.

“Ai kuwa cikin gaggawa ya saka aka kawo mana giya amma cikin rashin sa’arshi sai babu wanda ya daga wayar, sai ya fita da kanshi yaje ya karbo. Sai nayi gaggawar na dauki jakata na gudu, sai naga kayanshi a ciki, na cire na gudu daga dakin, na riga na saka a raina cewa zan fadi jarrabawarshi, ko a ranar jarrabawa sai da ya kara tunatar dani, haka kuwa na rubuta jarrabawar.

“Akwai zanga-zanga da aka gabatar a makarantar, wasu daga cikin malaman da suka jagoranci wannan zanga-zangar shugaban jami’ar duka ya dakatar da su. Ashe kuwa har da shi a ciki. Wani mutumi daban ya duba mana jarrabawar mu, ai kuwa na samu sakamako mai kyau. Allah ya taimake ni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here