Budurwa ta mutu watanni 2 bayan ta wallafa cewa za ta mutu a lokacin corona

0
491

‘Yan uwa da abokanan arziki na wata budurwa mai suna Chinenye George Sandra, sun shiga cikin hali na bakin ciki bayan samun labarin mutuwar ta da suka yi.

Budurwar mai shekaru 22 a duniya, kamar yadda hoton da aka buga na ranar binneta ya nuna, ta rasu a ranar 12 ga watan Yuni, 2020, bayan ta sha fama da jinya, inda kuma ake shirin binneta a ranar 3 ga watan Yuli.

Mutuwar Sandra dai ta zo wa yawancin mutanen da suka santa da kuma abokananta a Facebook a matsayin bazata kuma ta firgita su. Domin kuwa watanni biyu kacal kafin mutuwarta budurwar ta wallafa rubutu a shafinta dake nuni da cewa za ta mutu a wannan lokaci da aka hana zirga-zirga saboda coronavirus.

A cewar taL “Idan na mutu a wannan lokacin na hana zirga-zirga ba sai an kai ni an gwada ni a asibiti ba. Doya ce da manja da gari suka kashe ni.”

A wannan lokacin mutane da yawa sun dauki hakan a matsayin wasa, inda suka dinga yin sharhi na abin dariya. Bayan samun labarin mutuwarta, mutane da yawa sun yarda cewa akwai wani sirri dangane da harshen mutane.

Daya daga cikinsu kuwa, ita ce Ebeh Nnaemeka Ebeh, wacce ta hau shafin ta nuna bakin cikinta da rasuwarta, sannan kuma ta gargadi mutane akan abubuwan da suke cewa.

Ta ce: “RIP George Sandra. Ko dan yayi sauri nace RIP, maimakon Congratulations, amma ba zan iya cewa komai ba kan lamarin ubangiji. Allah yasa ki huta har abada a lahira.

“Kafin mutuwarta, Sandra tana sana’ar dafa abinci, kuma tana rayuwa cikin jin dadi. Amma ina fatan mutane za suyi hankali da harshensu, Akwai wani sirri kan abubuwan da muke fada. Kwata-kwata ko wata uku ba ayi ba da ta wallafa hakan gashi ta mutu.”

RIP GEORGE SANDRAWell it's too early to say RIP instead of CONGRATULATIONS, but I can't question the maker. May you…

Posted by Ebeh Nnaemeka Ebeh on Monday, June 29, 2020

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here