Budurwa ta gano cewa tana dauke da ciki ana saura awa hudu ta haihu

0
796

A lokacin da Lizzie Quah, mai shekaru 23 a duniya ta fara jin radadi a mahaifarta, tayi tunanin tana da ciwon koda ne.

Bayan ta isa asibiti ta firgita da aka gaya mata cewa tana dauke da ciki awa hudu kacal ya rage lokacin ta haihu.

Lizzie wacce take ‘yar Bloomingtoon, dake jihar Illinois dake kasar Amurka, ta wallafa labarinta a manhajar TikTok, inda ta bayyana cewa taje asibitin sanadiyyar ciwon da ya hana ta bacci a ranar 23 ga watan Yuni, 2019.

Lizzie Quah, a 23-year-old ballet instructor and client experience coordinator from Bloomington, Illinois, had no clue she was pregnant until four hours before she gave birth (Picture: Instagram/@lizzie_quaah)

Ta taba fuskantar matsala ta ciwon koda, hakan ya sanya tayi tunanin ta san abinda ya kamata tayi. Bayan kwantar da ita likita ya bayyana cewa zai bata maganin da zai rage mata radadin ciwo, amma ya ce zai gabatar da gwaji tukun don ya tabbatar da cewa ba ciki ne da ita ba.

Sai dai bayan gabatar da gwajin likitan ya gano cewa cikine da ita, kuma wannan ciwo da take ji ciwo ne na nakuda.

“Ashe lokacin ni har na fara nakuda ma ban sani ba cikin wannan daren,” cewar Lizzie a cikin bidiyon ta.

@lizziequah

I think I win this challenge 😂😳 *also she is safe she climbs everything. #crazypregancy #fyp #babiesoftiktok #storytime #putafingerdown #wildstory

♬ original sound – lizziequah

Sa’o’i kadan bayan gama gwaje-gwaje akanta, Lizzie ta sullubo jaririya lafiyayya.

Ta bayyana wannan haihuwa a matsayin babban tashin hankali a rayuwarta.

She had what seemed to be regular periods and only gained a little weight (Picture:: Instagram/@lizzie_quaah)

“Ban samu maganin nakuda ba, saboda koda an bani ma ba zai yi aiki ba, lokaci ya riga ya kure. Cikin radadi, ban san cewa haihuwa zanyi ba, ina ta tunanin namiji ne ko mace, lafiyayye ko marar lafiya, duka ina wannan tunanin ne a lokacin da nake wannan nakuda.”

Lizzie ta bayyana cewa bata fuskanci wata alama ta ciki ba, hakan yasa ba ta taba tunanin tana da jariri a cikinta ba.

Doctors gave her a physical exam before giving her medication for what she thought was a kidney stone – that’s how she discovered she was already in labour (Picture: Instagram/@lizzie_quaah)

Hatta jinin haila da mata suke yi Lizzie ta cigaba da ganin na ta, tana da ciwon zubar jini da idan mace tana dashi za tayi tunanin tana jinin haila ne idan yazo, hakan ya sanya tayi tunanin ita din ma jinin haila ne.

Lizzie’s pregnancy was high-risk, but she couldn’t have known (Picture: Instagram/@lizzie_quaah)

Duk da haka dai a karshe Lizzie tayi sa’ar haifo jaririyarta lafiyayya mai suna Winnie June.

Ta fara wallafa labarinta ne domin ta taimakawa mata da suke da yara kuma suke fama da rashin lafiya, inda take rokonsu da su kula da kansu matuka sannan kuma su nemi taimako a duk lokacin da suka ga cewa sun gaza.

Lizzie with her daughter, Winnie June (Picture: Instagram/@lizzie_quaah)

“Ko da kuna da ciki ko babu, mata sun cancanci girmamawa, fahimta da kuma goyon baya a lokacin haihuwa da kuma bayan haihuwa,” ta ce.

“Nayi sa’a dana samu tallafi a lokacin haihuwata, kuma har yanzu ina fama kalubale da ba a rasa ba. Ku tashi tsaye ku nemi tallafi, kada kuyi tunanin yin gwagwarmaya ku kadai.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here