Budurwa ta cakawa babbar kawarta wuka a kahon zuci kan ta bata shawara ta daina kwankwadar barasa

0
188

Wata budurwa ta cakawa kawarta wacce suke zaune a gida daya wuka akan ta bata shawara ta daina shan barasa.

Budurwar mai shekaru 27 mai suna Daria Alyabyeva ta cakawa Tatiana Nazarinova mai shekaru 31 wuka bayan tayi mata magana akan yawan shan giyar da take yi.

Kawayen guda biyu suna zaune tare ne a California shekaru da dama da suka wuce, amma yawan shan giyar da Alyabyeva take yi ya zama babbar matsala ga Tatiana.

Tatiana ta bayyanawa New York Daily News cewa tana so ta taimakawa Alyabyeva ta sama mata aiki, saboda duka sun fito daga kasar Rasha ne, tace tayi kokarin nema mata aiki, amma sai taje tana shan giya a lokacin da ake yi mata jarrabawar daukar aiki. Ta kara da cewa shan giyar na ta ya karu a wannan lokaci da aka killace kowa a gida saboda Coronavirus.

Tatiana ta tinkari kawartan a ranar 19 ga watan Afrilu, domin tayi mata magana akan shan giyar da take yi, amma cikin rashin sa’a sai ta nemi daukar rayuwarta. Ta ce tayi ta rokon Alabyeva akan ta kira ‘yan sanda lokacin da ta caka mata wukar, amma tayi kunnen uwar shegu ta gudu, daga baya ita ce ta rarrafa ta kira ‘yan sanda.

“Bai kamata tayi mini haka ba. Ni nake ciyar da ita, nake bata sutura, ni nake daukar nauyinta a koda yaushe. Na yiwa iyayena da kawayena alkawarin babu ni babu ita. Ba ta da hankali ko kadan.” cewar Tatiana.

‘Yan sanda sun cafko Daria kwanaki tara bayan tayi wannan aika-aika, inda aka yanke mata hukuncin kokarin aikata kisan kai. An tsare ta a tsibirin Rikers da kudin beli har dala dubu dari bakwai da hamsin ($750,000).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here