Budurcin ‘yarka kawai muke bukata ba kudin ka ba – Cewar ‘yan kungiyar asiri ga mahaifin wata yarinya a Bauchi

0
2647

Wasu da ake tunanin ‘yan kungiyar asiri ne sun sace wata budurwa mai shekaru 20 da suna Patience Emmanuel, wacce ke karatu a jami’ar jihar Bauchi a fannin magunguna, sannan suka bayyanawa mahaifin yarinyar cewa abinda suke bukata kawai shine budurcin ‘yarshi ba wai kudi suke so daga wajen shi ba.

Da yake bayyana yadda lamarin ya faru ga manema labarai, Mr Emmanuel Kushi, wanda yake ma’aikacin gwamnati ne, ya ce diyarshi wacce ya san cewa tana da cikakkiyar tarbiyya, ta bar gidan kaninshi a Rafin Zurfi dake jihar a ranar Laraba 24 ga watan Yuni, da niyyar za taje gidanshi ta dauko wani abu. Sai dai kuma bata je gidan nashi ba, kuma anyi ta nemanta a waya ba a sameta ba.

“Ranar Laraba, 24 ga watan Yuni, da misalin karfe 2 na rana, ta bar gidan kanina a Rafin Zurfi, inda ta sanar dashi cewa za ta zo gidana dake Kafin Tafawa, wanda yake da nisan kilomita hudu daga can. Ya ba ta dama da niyyar za ta zo ta dauki wani abu a nan.

“Da yamma matar kanina tayi ta kiranta a waya don tabbatar da kota iso nan lafiya, amma wayanta a kashe. Sun yi tunanin ta riga ta iso nan.

“Daga baya sun sake kira wayar a kashe. Washe gari ranar Alhamis da misalin karfe 1 na rana, matar kanina ta kirani a waya ta tambayeni akan mai yasa na hana Patience komawa can. Ta tambaya da fatan komai dai lafiya.

Na sanar da ita cewa ni ban ga Patience ba, saboda bata zo gidana ba. Ta yi mamaki sosai akan abinda nace, sai ta ce za ta kira kawarta ta tabbatar,” cewar Kushi.

Mr Kushi ya cigaba da cewa ya aikawa diyar tashi sako a wayarta, amma martanin da aka dawo masa da shi ya bashi mamaki sosai.

‘Kana tunanin za ka kara ganinta daga yau? Wawa.” Martanin da aka dawo masa dashi kenan.

Mr Kushi yace ya tafi gonarshi, a lokacin da ya dawo, sai ya sake iske sako da wadanda suka sace ‘yarshi suka turo masa, suka ce: “Baba, ‘yarka tana wajen mu (Black Axe Confretanity). Ba kudinka muke bukata ba, abinda muke so kawai shine budurcinta. Kada ka wahalar da kanka wajen nemanta.”

Mutumin ya ce har yanzu yana ta kokari ya gano sakon da mutanen suka sake aiko masa da wayar ‘yar tashi, inda suke nuna masa cewar ta mutu.

“Da misalin karfe 10:25 na safe, sun sake aiko mini da wani sakon, inda suka ce mini ta mutu. Muna ta kokarin kiran wayarta, amma a kashe. Abinda na sani shine ‘yata bata mutu ba. Na tabbata za ta dawo da ranta.” Cewar Mr Kushi.

Mr Kushi ya ce shi da danginsa gaba daya sun dage da addu’a, kuma sun tabbata da cewa har yanzu tana nan da raye, kuma za ta dawo gida cikin koshin lafiya.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Ahmed Wakil, ya ce ‘yan sanda tuni sun fara gabatar da bincike akan lamarin.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here