Bidiyo: Yadda ‘yan sanda suka cirewa wani batirin mota saboda ya hana su cin hanci

0
733

Wani dan Najeriya da ya wallafa rubutu a shafin Twitter, ya zargi ‘yan sandan da suke tsayawa kan babbar hanya da laifin cire mishi batirin mota saboda ya hana su cin hanci.

Bidiyon wanda ya yadu sosai a shafukan sadarwa, wanda aka sanyawa suna: “Bidiyon ‘yan sandan Najeriya da aka kama suna cirewa wani mutumi batirin mota, saboda yaki ya basu cin hanci a lokacin da suka tare shi akan babbar hanya.

A bidiyon dai an gano ‘yan sanda guda biyu suna rufe murfin gaban motar mai kirar Lexus, inda suka cire batirin suka nufi motarsu da suka ajiye a gefen hanyar.

Gaba daya dai an gano kimanin ‘yan sanda guda biyar a wannan waje.

Sannan kuma an jiyo mutumin wanda yake da motar yana yiwa ‘yan sandan magana duk da dai ba a nuno fuskarshi ba a cikin bidiyon.

“Kuna ganin dai irin abinda ‘yan sanda suke yi ko?” cewar direban motar wanda yayi magana da Turanci. “Kun cire mini batiri ko?”

‘Kudin da kuke so ku tara a wannan hanyar yau, idan kun tara shi ku canja mini suna.”

Har aka gama daukar bidiyon dai mai tsawon dakika 21, ba a jiyo ko daya daga cikin ‘yan sandan yana rokar cin hanci daga wajen direban motar ba.

Ya zuwa yanzu dai hukumar ‘yan sanda ta kasa ta bukaci a nemo mata rahoton inda wannan lamari ya faru da kuma lokacin da ya faru don taimaka musu wajen gabatar da bincike.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here