Bidiyo: Yadda wani fasinjan mota ya dinga shafa jikin wata budurwa suna tsakar tafiya a hanyar Abuja

1
44985

An kama wani mutumi a kyamara yana shafa jikin wata mata akan babbar hanyar Abuja zuwa Akure, babban birnin jihar Ondo.

Wata mai amfani da shafin Twitter mai suna @DanielFaithArts, ita ce ta wallafa bidiyon a shafinta, inda tace lamarin ya faru da ‘yar uwarta ne.

Ta ce ‘yar uwar tan da ta dauki wannan bidiyon ta kai karar mutumin zuwa wajen sojoji, amma daga baya sojan yace tayi shiru da bakinta ko kuma su riketa saboda mutumin yayi magana da shi da Hausa.

A cewar @DanielFaithArts, ‘yar uwarta tayi ihu a lokacin da mutumin yake taba ta, amma mutanen motar suka ce karya take yi, duk da wannan bidiyo da ta dauka.

Ga dai bidiyon da aka dinga wallafa a shafuka daban daban na Twitter:

A wani rahoton kuma, fitacciyar mawakiya DJ Switch ta bayyana yadda Kawunta ya dinga lalata da ita tun tana ‘yar shekara 11 a duniya.

A cewar mawakiyar, Kawun nata wanda yake Malamin coci ne yayi mata barazanar ba zai saka mata albarka ba matukar ta sanar da wani abinda yake yi mata.

A karshe ta tsinewa duk wanda yake yiwa wasu fyade wala Allah mace ko namiji, ta ce irin wannan mutanen basa cancanci rahamar Allah ba.

KU KARANTA: Tun ina ‘yar shekara 11 Kawuna yake lalata dani, wanda yake Malamin coci ne a lokacin – DJ Switch

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here