Bidiyo: Yadda saurayi ya kama budurwarsa da kato tsirara a otel suna lalata

0
525

Wani matashin saurayi da yake shirin bawa budurwarsa mamaki ta hanyar hada mata gagarumin bikin ranar haihuwarta a wani otel a garin Benin, ya shiga tashin hankali bayan ya kamata dumu-dumu da wani katon saurayi a cikin wannan otel din.

Rahotannin da muka samu sun nuna cewa budurwar ta tambayi saurayin ya bata kudi za tayi shagalin bikin ranar haihuwartan, amma sai ya bayyana mata cewa shi ba shi da kudi da niyyar ya bata mamaki.

A ranar bikin haihuwar ta din, bayan ya kammala hada komai a otel din dake Benin, sai ya wuce zuwa gidansu budurwar domin ya dauko ta ya kawo ta otel din, sai dai ya tarar da bata nan a lokacin da ya isa gidan.

Sai dai kuma, ya gano inda ta tafi bayan ya bawa mahaifiyarta cin hanci, ai kuwa tana gaya masa ya gane cewa tana otel din da ya shirya mata wannan hidima.

Abin mamaki bayan barin gidansu yayi tunanin ko ita ma taji labarin abinda yake hada mata ne ta riga shi zuwa otel din.

Sai dai bayan zuwan shi ya tarar lamarin ba haka yake ba, domin kuwa ya tarar da ita da wani saurayi ne zigidir a wani dakin otel suna lalata.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here