Bidiyo: Yadda nakuda ta kama mawakiya a lokacin da take tsakiyar waka a bainar jama’a

0
1085

Wani bidiyo da yake ta yawo a shafukan sadarwa, ya nuna yadda wata mawakiya ‘yar kasar Uganda wacce keda tsohon ciki ta fara nakuda a lokacin da take waka a bainar jama’a.

Mawakiyar na tsakiyar rawa da a lokacin da taji zafi mai tsanani na nakuda ya taso mata, cikin nuna alamu na jin ciwo tayi ihu ta jefar da lasifikar.

Ta durkusa kasa ta dafe cikin nata kafin daga baya ta kira masu lura da zirga-zirgar mutane a wajen suka taimaka mata suka dauke ta.

Sai da aka samu mutane biyu masu karfi daga cikinsu suka iya samu suka dauke ta aka wuce da ita asibiti.

Bidiyo: Naija Life

A daya bangaren kuma a jiya muka kawo muku rahoton budurwa ‘yar kasar Amurka da bata san cewa tana dauke da tsohon ciki ba sai bayan ana saura awa hudu ta haihu.

Budurwar ta bayyana cewa tayi tunanin ciwon koda ne take dashi shi yasa lokacin da taji ciwo ya taso mata ta nufi asibiti domin likita ya bata magani.

Amma abin mamaki shine, lokacin da ta isa asibitin tasha mamaki bayan likita yace mata ciki ne da ita kuma wannan ciwo da take ji ciwo ne na nakuda.

Karanta rahoton: Budurwa ta gano cewa tana dauke da juna biyu ana saura awa hudu ta haihu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here