Bidiyo: Yadda magidanci ya yanke jiki ya fadi bayan ya gama zina da matar aure a gidansa

0
1914

Wani mutumi da ba a bayyana ko waye ba ya fadi ranga-ranga bayan ya gama zina da matar aure a jihar Legas.

Matar wacce wasu mutane dake zaune a yankin suka dinga yi mata tambayoyi a lokacin da lamarin ya faru, ta bayyana cewa ita matar aure ce, amma ta ce tayi dana sanin kwanciya da shi.

Matar ta bayyana cewa tana zaune a yankin Mutatiri dake Cele a jihar Legas.

Ta ce ta tuna lokacin da take sanar da danta cewa za ta je ta siyo abu kafin ta bar gida, inda ta dora laifin a kanta.

Daga baya an garzaya da mutumin zuwa asibiti a kan babur domin ceto rayuwarsa.

Ga dai bidiyon yadda lamarin ya kasance a kasa:

A wani labari makamancin haka kuma Press Lives ta kawo muku rahoton mutumin da ya dinga shafa jikin wata budurwa a cikin motar haya a yayin da suke tafiya.

An ruwaito cewa lamarin ya faru akan babbar hanyar Abuja zuwa Akure ne, inda budurwar ta bayyana cewa ta kai karar mutumin ga sojoji amma kuma basu dauki wani mataki akan lamarin ba.

Ta ce sojan da ta sanar da abinda mutumin yake yi mata yace tayi shiru da bakinta ko kuma su tsare ta saboda mutumin yayi magana da Hausa.

Ga dai labarin: Bidiyo: Yadda fasinjan mota ya dinga shafa jikin budurwa a lokacin da suke tsakar tafiya a hanyar Abuja

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here