Bidiyo: Yadda aka sha dambe tsakanin wasu manyan mutane kan budurwa a tsakiyar titi

0
119
  • Bidiyon wasu mutane guda biyu da suka dan manyanta na ta yawo a shafulkan sadarwa, bayan an dauke su suna dambe a bainar jama’a
  • An bayyana cewa mutanen suna yin wannan rikici ne akan mace ne
  • Bayan an yi musu barazanar za a wallafa bidiyonsu a shafin sadarwa na Facebook sun daina fadan a karshe

Wasu manyan mutane sun dambatu akan tsakiyar titi kan wata mata da kowanne a cikinsu yake so.

A wani bidiyo da aka wallafa a kafafen sadarwa na yanar gizo, an gano duka mazan suna kaiwa juna naushi a tsakiyar titi inda mutane da yawa suka tsaya suna kallon ikon Allah.

Duk da cewa mutane sun saka su a gaba suna kallo, ko a jikinsu, domin kuwa basu nuna alamar zasu daina damben ba.

To sai dai daga baya bayan an yi musu barazanar za a yada bidiyonsu a shafukan sadarwa na yanar gizo sun tsaya da damben.

A cikin bidiyon dai an jiyo muryar mutane na yiwa masu damben magana cikin yaren yarabanci akan su daina rikicin wanda suka bayyana akan mace ne.

Ga dai bidiyon dai a kasa:

View this post on Instagram

Two men filmed fighting over a woman.

A post shared by Lindaikejiblog (@lindaikejiblogofficial) on

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here