Bidiyo: Yadda aka gano gawa tana dagowa mutane hannu daga cikin akwati yayin da ake shirin binne ta

0
195
  • Bidiyo ya nuna yadda gawa take dago hannu daga cikin akwati a lokacin da ake shirin binne ta
  • Lamarin wanda ya faru a kasar Indonesia ya bar mutane cikin mamaki, inda suke ganin anya wannan mutumi ya mutu kuwa
  • Wasu kuwa cewa suka yi mutumin yana da rai kokari yake ya fito daga cikin akwatin, inda wani kuma yace zai iya yiwuwa bera ne ya shiga cikin akwatin

Wani bidiyo ya nuna yadda gawa take dagawa mutane hannu daga cikin akwati a lokacin da suke shirin binne ta.

Wannan abu wanda daya daga cikin wadanda suka je binne gawar ya dauka, a lokacin da ake shirin binne mamacin a birnin Manado dake yankin arewacin Sulawesi cikin kasar Indonesia, a ranar 5 ga watan Mayu.

A yayin da fasto yake addu’a tare da ‘yan uwan mamacin, an gano hannu yana motsi daga cikin gilashin akwatin gawar a yayin da mutanen ke bankwana da shi.

Wannan bidiyo dai ya bar mutane da dama suna tunanin shin mutumin ya mutu ne ko kuwa yana da rai?

“Kwarai kuwa ya dago hannu, watakila yana da rai yana kokarin ya fito daga cikin akwatin ne,” cewar wata mai suna Yunita Ouwa.

Wani kuwa cewa yayi zai iya yiwuwa ba hannu bane ma, zai iya yiwuwa bera ne.

Sai dai wani sabon bincike da aka gabatar a watan Satumbar shekarar 2019, wanda Medical News ta ruwaito ya nuna cewa gawar mutum na iya motsi da kanta bayan mutuwa.

Masu binciken a jami’ar Queensland dake Rockhamton cikin kasar Australia, wadanda suke bincike akan yadda gawar dan adam take bayan mutuwa, sun bayyana cewa gawar na iya canja yanayin wajen da take ba tare da wani ya taba ta ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here