Bidiyo: Ta daure danta a cikin buhu tsawon kwana 4 babu ci ba sha saboda aljanu sun shiga jikinshi

0
280
  • An kama wata mata da ta daure yaronta mai shekaru goma a cikin buhu na tsawon kwana hudu
  • Matar mai suna Iya Ayo ta kulle yaron a cikin buhun ne akan zargin yana da aljanu
  • Ta ce aljanu ne dashi da suke saka shi yake yiwa mutanen yankinsu sace-sace shi yasa ta kulle shi

Jami’an hukumar ‘yan sanda sun cafke wata mata mai suna Iya Ayo, da laifin daure danta mai shekaru 10 a cikin buhu, sannan ta kulle shi a cikin daki na tsawon kwanaki hudu a kauyen Fesojaye dake Owode cikin jihar Osun.

Matar an ruwaito cewa ta daure dan nata a ranar Alhamis din da ta gabata, sai a ranar Lahadi 16 ga watan Mayu daya daga cikin makwabtansu ya jiyo kukan yaron yana neman taimako. Mutumin cikin gaggawa ya sanar da manyan unguwar, su kuma suka sanar da ‘yan sanda, an kama matar a karshe inda shi kuma dan nata aka sake shi.

Da aka gabatar da bincike a kanta, Iya Ayo, wacce ta rabu da mahaifin yaron, ta ce aljanu sun kama dan nata inda suke saka shi yana sacewa mutane kudi.

Da ake tabbatarwa da jaridar Linda Ikeji yadda lamarin ya faru, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Yemisi Opalola, ya ce sun kama matar kuma ta sanya hannu akan takardar cewar baza ta kara cin zarafin yaron ba.

Opalola ya ce ya zuwa yanzu suna kokarin nemo mahaifin yaron domin a danka masa yaron, inda yace ‘yan sanda kuma suna kokari akan lamarin yaron.

Ga dai bidiyon lokacin da ake ceto yaron:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here