Bidiyo: Matashin manomi ya kera mota a garin Jama’aren jihar Bauchi

0
519

Wani matashi mai suna Auwal Hassan dan garin Jama’are dake jihar Bauchi ya kirkiri motar hawa mai dan karen kyau.

Akwai dubunnan matasa a Najeriya masu basira dake kere-kere a Najeriya, sai dai mafi yawa basirar ta su bata samun tagomashi wajen kara bunkasa abubuwan da suka sanya a gaba.

Auwal ya ce: “Abinda ya bani sha’awa gaskiya shine, ni kaina na kasance mai sha’awar mota ne, kuma ni bani da kudin sayen mota, shine yasa na fara tunanin yadda zanyi na kera tawa, hakan ya jawo hankalina har na fara neman yadda zanyi na sayi inji, tayoyi da sauransu, sai gashi kuma Allah da ikonsa komai ya kammala.

Matashin ya nuna dalla-dalla yadda ya tsara motar tashi daga kan byan motar har zuwa cikin motar da yadda ya sanya inji da sauran su.

Kasancewar mutane masu fasahar kere-kere irin wannan suna bukatar tallafi da zai bashi damar bunkasa sana’arsa, Auwal ya ce yana amfani da sana’ar da yake yi ta noma wajen samun kudin bunkasa fasahar ta sa.

“Wani lokacin sai na bari da damina idan nayi noma na sayar da kayan gona, sai nayi amfani da kudin wajen cigaba da kera motar, hakan ya sanya aikin ya dauki lokaci mai tsawo.

Matashin ya ce yana da sako ga ‘yan uwansa matasa akan yadda za su gina rayuwar su.

“Gaskiya sakon da nake dashi ga al’umma, musamman mu matasa, shine ayi kokari a nemi na kai, kuma a lura da sana’a, sana’a tana da muhimmanci sakamakon sana’ata ne nima na samu na kera wannan mota.”

Kamar yadda alkaluman bincike suka nuna tsarin tattalin arziki siyasa, na daga cikin abubuwan da suka dabaibaye nahiyar mu ta Afrika ya sanya koda yaushe muka zamanto a baya.

https://www.facebook.com/watch/?v=267019687719123

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here