Bidiyo: Mata mai ciki ta fashe da kuka bayan wani bawan Allah ya bata kyautar naira miliyan 4

0
581

Wata mai ciki da Allah ya taimaka ta samu goma ta arziki daga wajen wani mutumi da ta hadu dashi a titi babu dangin iya babu na baba, inda ya bata dala dubu goma ($10,000) kimanin naira miliyan hudu kenan a kudin Najeriya.

Mutumin ya bata kudin ne inda ya bayyana mata ta kula da kanta da dan dake hannunta da kuma jaririn da za ta haifa.

Mutumin dai ya tsaya ne ya fara yiwa matar tambayoyi, inda ta bayyana masa cewa tana da ciki, inda daga nan ya fito da kudin ya bata.

Matar wacce mamaki ya cika ta ta fashe da kuka a take a wajen, saboda ta kasa yadda akan cewa mutumin da gaske yake, mutumin ya nuna mata da gaske yake yi, inda daga baya ta karbi kudin.

https://www.facebook.com/watch/?v=2693053464302894

Duk da cewa irin wannan kyauta ta bazata ba komai bace a kasashen Turawa, amma wannan ta fita daban, domin a kasashen sau da yawa zaka ga mutum ya je ya siyo abinci ko abin sha kala-kala yana bi yana bawa mutanen da ya hadu da su a titi.

Bidiyon wanda aka wallafa a shafin Facebook ya burge mutane da dama inda da yawa suke mamakin shin dama mutumin a shirye ya fito da niyyar kyautar da wannan kudin ko kuwa a wannan lokacin ya yanke shawarar ba ta kyautar kudin.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here