Likitoci a kasar Indiya sun cika da mamaki bayan sun ciro cajar waya mai tsawon gaske daga cikin wani mutumi mai shekaru 30.
Mutumin wanda ake zargin yana da tabin hankali, ya bayyanawa likitocin cewa ya hadiye cajar wayar ne daga baki, amma kuma likitocin sun gano cewa cajar ta shiga cikin shine ta ga kofar azzakarinsa.
A wani rubutu da daya daga cikin likitocin da suka yiwa mutumin aiki ya wallafa a shafinsa na Facebook, mai suna Wallie Islam, ya ce mutumin ya dinga yi musu kukan cewa yana jin ciwo a cikinsa, sannan ya gaya musu cewa ya taba hadiye cajar waya.

“Bayan shafe shekaru 25 ina yin tiyata, nayi mamaki dana ga irin wannan,” cewar Islam a rubutun da ya wallafa ranar Alhamis 4 ga watan Yuni.
“Nayi masa tiyata ban samu komai a cikinsa ba, amma kuma mun gano cajar waya a cikin mafitsararsa…dukkan ku zaku yi mamakin daga inda ta samu shiga wannan waje (ta samu shiga taga cikin kofar azzakarinsa),” cewar Islam.
Mutumin ya bayyanawa likitocin cewa ya hadiye cajar daga baki ne, amma gaskiyar magana ya sanyata daga azzakarinsa ne.
“Shekara ta 25 ina yin tiyata, amma wannan shine karo na farko dana taba ganin abu makamancin haka,” cewar Islam.
“Ya zo gare mu kwanaki biyar bayan ya hadiye wayar. Ya sanar damu cewa ya hadiye wayar ne, amma gaskiyar magana ba haka bane, bamu taba tunanin babban mutum irinsa zai yi karya ba,” cewar Islam.
Yanzu haka dai mutumin yana samun sauki, kuma bayan gwaji a kanshi mun gano cewa lafiyarshi lau, ya sanya wayar ne cikin jin dadi.
Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:
Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa
Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com