Bidiyo: Jarumar Bollywood Sushmita Sen dake bin addinin Hindu ta karanta Al-Qur’ani mai girma cikin murya mai dadi

0
155

Fitacciyar jarumar fina-finan Indiya na Bollywood Sushmita Sen, wacce ta lashe gasar mace mafi kyau a duniya a shekarar 1994. Ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Twitter inda take raira karatun Al-Qur’ani.

A bidiyon an nuno ta tana karatun tare da daya daga cikin ‘yarta inda ita ma take raira karatun na Qur’ani tare da mahaifiyarta.

Haka kuma ta yiwa mutane addu’a da dama dama wadanda ba Musulmai ba duk tayi musu a wannan lokaci na Coronavirus.

Mutane da yawan gaske sun kalli wannan karatu na ta da ta wallafa a shafinta na Twitter, inda suka dinga yaba mata. Ganin cewa jarumar ba wai addinin Musulunci take koyi da shi ba.

Wannan ba shine karo na farko ba, a shekarar 2017, a kasar Dubai, Sushmita Sen ta karanta Al-Qur’ani mai girma a lokacin da take hira da manema labarai a Sharjah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here