Bidiyo: Ana neman ma’aikaciyar asibiti da tayi rawar iskanci da kayan aiki a jikinta ruwa ajallo

0
263
  • An bayar da umarnin nemo wata ma’aikaciyar lafiya a kasar Ghana a duk inda take
  • Hakan ya biyo bayan wani bidiyo da tayi tana rawar iskanci a cikin kayan aikin asibiti
  • An bukaci duka ma’aikatan lafiya da su guji irin wannan dabi’a musamman idan suna sanye da kayan aiki

Wata ma’aikaciyar asibiti ‘yar kasar Ghana da bidiyonta ya dinga yawo a wannan makon tana rawar iskanci da kayan aikin asibiti a jikinta, an bukaci a nemota a duk inda take.

A bidiyon, ma’aikaciyar asibitin an nuno ta tana rawar iskanci, inda shi kuma wani yazo daga bayanta yake taya ta abinda take yi.

Bayan fitar bidiyon mutane da yawa sun dinga Allah wadai da cin mutuncin kayan asibiti da tayi da kuma shi kanshi aikin nata da ta tozarta.

Bayan maganganu da mutane suka yi tayi, sai lamarin yaje kunnen kungiyar ma’aikatan lafiya ta kasar Ghana, inda suka bukaci duka mutanen da suke da masaniya akan wannan matar da su taimaka su bayyana ko wacece domin ayi mata hukunci.

A karshe sun gargadi ma’aikatan lafiya da su guji irin wannan dabi’a musamman ma idan suna sanye da kayan aiki, don kare martabar wannan aiki.

Ga dai bidiyon rawar iskancin da ma’aikaciyar asibitin tayi a kasa:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here