Bidiyo: An nuno ma’aikatan jirgin sama suna turin jirgi a lokacin da yaki tashi a Najeriya

0
2044

Wani bidiyo da yake ta yawo a Najeriya ya nuna lokacin da wasu ma’aikatan filin jirgin sama suke tura jirgin sama wanda ake tunanin ya samu matsala suna so ya tashi.

Mutumin dan Najeriya da ya dauki wannan bidiyo, an jiyo shi yana cewa “Abin mamaki baya karewa a duniya.” Wannan dai ya samo asali ne saboda karancin abubuwan more rayuwa a kasar.

Mai amfani da shafin Facebook, Rena Napoleon wanda ya wallafa wannan bidiyo a shafinsa na Facebook yayi rubutu kamar haka:

“Ya Allah ka zo ka raba Najeriya kowa ya kama gabansa saboda tuni Najeriya ta riga ta mutu, tura jirgin sama saboda ana so ya tashi? Chaaii irin wannan abu yana faruwa a Najeriya ne kawai. Ina jin tausayin mutanen dake cikin wannan abu da ake kira da suna jirgi.”

Abeg God come and split Nigeria make everybody go there own country and change identity cause Nigeria is dead and gone…..pushing ✈️ ✈️ plane to start ? Chaaii only in Nigeria ..I pity people that will board this wheelbarrow called plane for travelling…

Posted by Rena Napoleon on Tuesday, June 9, 2020

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here