Bidiyo: An kama Alhaji tsirara haihuwar uwarsa zai yi luwadi da saurayin da ya yiwa alkawarin zai kai kasar waje

0
5270

Wani mutumi da ake tunanin dan luwadi ne ya shiga hannun wasu mutane, a lokacin da yake kokarin yin luwadi da wani mutumi marar a Ikpoba Hill dake Benin city cikin jihar Edo.

Mutumin da aka bayyana sunansa da Alhaji yana so ya kwanta da saurayin a matsayin ramuwa akan babbar motar tirela da ya siya masa.

A cewar saurayin, Alhajin yayi masa alkawarin zai kai shi kasar waje ya dora shi akan harkar kasuwanci na safarar miyagun kwayoyi, inda shi kuma ya amince.

Ya bayyana cewa Alhajin ya bayyana masa cewa za a dinga boye miyagun kwayoyin ne a cikin duburarsa. Da aka tambayeshi daga yaya hakan za ta faru sai ya bayyana cewa Alhajin ne zai koya masa.

Saurayin ya fara rashin lafiyar ne a lokacin da Alhajin ya kira shi ya bayyana masa cewa zai zo gidansa.

Da ya isa gidan ya bayyanawa saurayin zai koya masa yadda zai boye kwayar a cikin duburarsa. Abin mamaki kawai sai yaga Alhajin yana matsowa kusa da shi har yana umartarshi da ya cire wandonsa.

Ya ce Alhajin yayi kokarin yin luwadi da shi a wannan lokacin, sai dai kuma hakan bai yiwu ba saboda azzakarin Alhajin yaki yin aiki a lokacin.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here