Bayyanar wasu hotunan bikin Asiya Ahmad da TY Shaba a matsayin miji da mata kwanan nan ya tayar da kura a kafafen sadarwa, har wasu na tunanin ko dai jarumin ya auri kanwar tsohuwar matarsa Samira Ahmad ne.

Sai dai daga baya an gano cewa ashe an shirya bikin ne don daukar wakar ‘Mu yo biki amarya’, wanda kamfanin Bluesound Records ya shirya.

Ganin yadda lamarin ya ja hankalin masu kallo, mujallar fim ta ji ta bakin TY Shaba, dangane da dalilin sa na shirya wakar tare da jaruma Asiya Ahmad (Mai Kyau). Amsar da ya bayar ita ce: “To, gaskiya ne kamar yadda kuka tambaye ni, wadda muka yi wannan wakar da ita Asiya Ahmad ce, kanwar Samira. Sai dai abin da mutane ya kamata su sani shine, ita Asiya Ahmad tana matsayin jarumar fim ne, ni kuma jarumi ne, don haka za mu iya fitowa a fim daya a matsayin mata da miji.

“Babu wani abu idan tsarin labarin yayi daidai mu fito tare, to fitowar mu da ita ba wani abu ba ne.

“Kuma kamar yadda jama’a su ka gani a wakar, tun kafin mu fara aiki sai da mu ka tsara mu ka nemi wadda za ta fito a matsayin amarya, don haka da mu ka gwada Asiya sai mu ka ga tayi daidai da wannan mataki, haka ya sanya muka saka ta.

“Saboda haka jama’a su sani, yanayin tsarin wakar ne ya ba mu damar mu fito ni da ita a matsayin ango da amarya.”

Daga karshe TY Shaba, ya yi kira ga jama’a da su rinka bambance rayuwar fim da ta zahiri.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here