Bature ya bawa abokinshi bakar fata damar yiwa matarsa ciki saboda yana jin kunyar zaman shi Bature

1
8518

Wani Bature dan birnin Portland dake kasar Amurka ya bawa abokinshi bakar fata dan nahiyar Afrika damar yiwa matarsa ciki saboda yana so su haifi bakar fata, akan jin kunyar zaman su Turawa.

Mutumin mai suna Peyton Wesley mai shekaru 43, ya roki abokin nashi bakar fata ya kwanta da matar tasa saboda a cewarsa ya gaji da jin kunyar zaman shi Bature.

Tyrone DeAndre mai shekaru 36, wanda yake aiki a kamfanin siminti, inda Wesley yake a matsayin manaja, ya ce yayi mamaki sosai akan wannan bukata ta shugaban nashi, amma yace daga baya ya amince.

“Ba kowanne lokaci bane zaka samu shugabanka ya bukaci ka yiwa matarsa ciki,” cewar Tyrone DeAndre da ya sanar da manema labarai.

“Da farko nayi tunanin ko ya haukace ne. Saboda ban wani san shi ba sosai. Amma ya ce mini ni kadai ne bakar fata da ya sani. Daga ganinshi ya matsu” ya ce.

“Idan har ba zan biya kudin kula da yaron ba shikenan ba matsala, na gaya masa.”

Duk da dai cewa Peyton Wesley bai bayyana ainahin nawa ya bawa Tyrone DeAndre ba, ya dai bayyana cewa kudade ne masu yawa.

“A matsayina na Bature komai ya zo mini da sauki, na fito daga dangi masu rufin asiri, kuma na samu damar samun komai na rayuwata ya tafi yadda nake so.” ya bayyanawa manema labarai.

“Amma ni na san akwai matsala, na kasa daina tunani akan wannan dukiyar tawa, ina so na bawa wani damar samun wannan dama da nake da ita shima ya samu rayuwa mai kyau, saboda kawai an haife ni da irin wannan fatar,” ya ce.

“Zai zama wani iri ace ka biya wani domin ya zama mahaifin danka, amma babu wani kudi da zai iya fitar da damuwar da nake dauke da ita ta shekaru daruruwa akan yadda Kakannin mu suka mayar da bakar fata bayi da kuma rashin adalcin da ake yi musu,” ya ce.

Tyrone DeAndre yayi aiki a kamfanin na watanni kadan ne kafin Wesley ya zo masa da wannan bukata mai abin mamaki, Wesley ya ce DeAndre da matarsa sun samu fahimtar juna sosai, inda yake fatan DeAndre zai yi kokari wajen zama wani bangare na dansa a nan gaba.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here